A cewar rahoton, kasashen biyu sun kasa cimma matsaya kan batun tsaro, yayin da mai shiga tsakani na Afirka ya dage zaman taron don baiwa sassan biyu damar kara tuntubar juna.
Jaridar ta ruwaito Omer Dahab, mai magana da yawun tawagar Sudan, yana mai cewa, tawagar sasantawa ta Sudan ta ki amincewa da shirin da tawagar Sudan ta kudu ta gabatar dangane da dage dokar-ta-bacin da aka sanya kan iyaka tare da dawo da wakilicin diflomasiya tsakanin kasashen biyu.
Dahab ya ce Sudan ta yi na'am da muhimmancin wannan bukata na dage dokar-ta-baci da musayar jakadu tsakanin kasashen biyu, amma wadannan ba su da nasaba da batun tsaro, kuma fita ne daga da'irar kokarin shimfida ginshikan tabbatar da tsaro da zaman lafiya tsakanin kasashen biyu kafin su tattauna sauran batutuwan da ba su warware ba. (Ibrahim Yaya)