A yayin taron na shugabannin kasashen kungiyar BRICS, kasar Afrika ta kudu za ta daukar matakan kalubalantar kudin dalar Amurka da su ka mamaye harkokin kudi na duniya, musamman ta bangaren kasuwanci da zuba jari a cikin kasuwanin kasashe masu tasowa, kamar yadda jaridar kasar Afrika ta kudu mai sunan City Press ta sanar a ranar Lahadi.
Yin amfani da kudin kasar Sin a maimakon dalar Amurka zai taimakawa kwarai wajen samun riba ga kasashen Afrika ta hanyar kasuwancin da kasashen kungiyar BRICS ta bangaren rage tsadar hajoji, da fannin rage sarkakiya a cikin sha'anin kasuwanci, kamar yadda bankin Standard, wato bankin da ya fi girma a kasar Afrika ta kudu ya sanar a game da wani bincike da ya gudanar.
A ranar Alhamis da ta gaba, gwamnatin kasar Afrika ta kudu ta furta cewa, shugaban kasar Jacob Zuma zai halarci taron koli na kungiyar BRICS karo na 4 da zai gudana daga ranar 28 zuwa 29 ga watan Maris a New Delhi, babban birnin kasar Indiya, taron na da taken "Am fanin huldar da ke tsakanin kasashen BRICS wajen tabbatar da daidaito, tsaro da bunkasar duniya". Kungiyar BRICS ta kumshi kasashen da su ka hada da Brazil, Rasha, Indiya, Sin da kuma kasar Afrika ta kudu da suka fito daga cikin kasashen duniya masu tasowa ta fannin tattalin arziki. (Abdou Halilou)