Yin Chengji ya kuma nuna cewa, a farkon rabin shekarar nan, kasar Sin ta ci gaba da fitar da manufofin da za su iya samar da karin guraben aikin yi a kasar, musamman ma ga wadanda suka kammala karatu a jami'o'i, da kuma wadanda suke cikin mawuyacin hali a birane da dai sauransu.
Bugu da kari, bisa labarin da aka samu, ayyukan samar da hidimomin kasar Sin na ci gaba da bunkasa cikin sauri. Hakan ya ba da taimako sosai wajen samar da karin guraben aikin yi a kasar, musamman ma cikin wasu sabbin ayyukan hidimomi, da kuma ayyukan hidimomi da suka shafi intanet da dai sauransu. (Maryam)