Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta bayar da rahoto cewa, an kyautata tsarin samar da guraben aikin yi a kasar Sin.
Rahoton ya ce, ya zuwa karshen shekarar 2011, yawan Sinawa da suka samu guraben aiki yi ya haura miliyan 700 wato ke nan adadin na karuwa da miliyan 3.489 a ko wace shekara inda an kwatanta shi bisa na shekarar 2001.
Ban da wannan kuma, rahoton ya ce, saboda an kyautata tsarin birane da na masana'antu, kuma bisa manufofin da suka shafi aikin samar da guraben aikin yi da gwamnatin kasar Sin ta gabatar, manoma da dama wadanda ba su da aikin gona su samu aikin yi a wasu fannoni na daban, lamarin da ya taimaka waje raya birane da gundumomi yadda ya kamata.
Sanin kowa ne cewa, samar da guraben aikin yi matsala ce da kasashen duniya suke fuskanta. A matsayin kasa da take da yawan jama'a a duniya, Sin ta fi fama da wannan matsala. A cikin shekarun nan da suka gabata, mutane masu dimbin yawa wadanda suke da shekaru tsakanin 24-30 da haifuwa na neman samun aikin yi, an warware wannan batun yadda ya kamata bisa karuwar tattalin arziki cikin sauri da kuma manufofin tallafi wajen samar da guraben aikin yi.(Amina)