in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen da suka samu aikin yi a Afrika ta kudu ya karu
2011-03-24 10:00:41 cri

Ranar Laraba 23 ga wata, hukumar kididdiga ta kasar Afrika ta kudu ta bayar da wata kididdiga inda ta ce, yawan mutanen da suka samu aikin yi a kasar a karshen watanni uku na shekarar 2010 ya karu sosai. Bisa kididdigar da aka bayar, an ce, a cikin wadannan watanni, yawan mutanen da suka samu aikin yi a sauran fannoni ban da sha'anin noma ya kai miliyan 8.155 wanda ya karu da kashi 1.2 cikin 100 bisa na watannin Yuli, Agusta da Satumba na shekarar 2010, kuma ya karu da dubu 93 wato kashi 1.1 cikin 100 bisa na makamancin lokaci na shekarar 2009.

Wata kafar yada labaru ta kasar ta ba da labarin cewa, a cikin farkon watanni biyu, sabbin mutanen da suka samu guraben aikin yi ya kai dubu 157. Gwamnatin kasar za ta kara samarwa kamfanoni masu zaman kansu manufofin gatanci a fannoni hakar ma'addinai, sana'ar kere-kere, gina manyan ayyukan more rayuwa, samar da abinci, yawon bude ido, tufafi, sana'ar samar da kayayyaki da dai sauransu, domin taimakawa wadannan kamfanoni wajen habaka su ta yadda za su samar da guraben aikin yi masu dimbin yawa.(Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China