in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na shirin samar da karin guraben aikin yi sama da miliyan 9 a shekarar 2013
2012-12-19 15:56:49 cri
Ofishin ministan kwadago da ba da tabbaci ga zaman rayuwar jama'a na kasar Sin, ya yi wani zaman taro a ranar 18 a nan birnin Beijing, inda ministan wannan ma'aikata, Yin Weimin ya gabatar da makasudin da za a cimma a shekara mai zuwa wato shekarar 2013 an cewa, za a samar da karin guraben aikin yi kimanin miliyan 9 da kuma ganin an tabbatar cewa yawan mazauna garuruwan marasa aikin yi ba zai haura kashi 4.6 bisa dari ba.

Yin Weimin ya ce, daga watan Jarairu zuwa Nuwamba na bana, yawan mutane daga birane ko kauyuka daban-daban da suka samu guraben aikin yi ya kai sama da miliyan 12, yayin da yawansu da suka sake samun aikin yi ya kai miliyan 5.25, amma kuma duk da nasarar da aka samu a wannan fanni, matsakaicin yawan mutanen dake neman guraben aikin yi a ko wace shekara ya zarce miliyan 24, abin da ya kasance wani babban kalubale da Sin za ta fuskanta nan gaba.

Ban da haka, Yin ya ce, ya kamata Sin ta kara karfin ba da horaswa da sa kaimi ga wadanda suke samu ilmi mai kyau ta yadda za su gudanar da aikinsu yadda ya kamata a guraben da suka dace, domin tabbatar da burin da Sin ta sanya gabanta wato zama wata kasa mai karfi wajen mallakar kwararru masu dimbin yawa kafin shekarar 2020. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China