Bisa labarin da muka samu daga ma'aikatar kula da harkokin ma'aikata da samar da tabbaci ga zaman rayuwar al'umma ta kasar Sin, an ce, akwai muhimman dalilai uku wadanda suka sanya karuwar adadin yawan mutanen da suka samu ayyukan yi a bara. Na farko shi ne ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, na biyu, akwai manufofi daban-daban da aka aiwatar don kara samar da guraban ayyukan yi ga jama'a. Na uku kuwa shi ne, kara kokarin tallafawa wadanda suka bukaci taimako yayin da suke neman ayyukan yi.(Murtala)