Kwanan baya, ma'aikatar kula da harkokin cinikayya da saka jari ta Nijeriya ta sanar da cewa, za ta samar da guraben aikin yi kimanin miliyan 3.1cikin shekaru 3 masu zuwa, kuma an kimanta cewa, bankuna za su kara samar da guraben aikin yi kimanin miliyan 1, kana, ma'aikatar cinikayya za ta kara samar da gubaren aikin yi kimanin miliyan 2.
Yanzu, akwai mutanen da yawansu ya kai sama da miliyan 12 da suke fama da matsalar rashin aikin yi, kuma yawan mutanen da ba su da aikin yi ya karu daga kashi 13.1 cikin 100 a shekarar 2005 zuwa kashi 19.7 cikin 100 a shekarar 2009, kana cikinsu yawan matasa a biranen da ba su da aikin yi ya kai kashi 49.9 cikin 100 a shekarar 2009.(Bako)