Wannan jami'i ya shedawa manema labaru a gun taron shekara-shekara na majalisar ministoci da aka yi a wannan rana cewa, z a tattauna kan yadda za a samu bunkasuwar tattalin arziki da samar da guraben aiki da sauransu batutuwan da suka shafi zaman rayuwar jama'a a taron wannan karo na tsawon kwanaki hudu. Shugaban kasar Jacob Zuma zai gabatar da rahoton halin da kasar ke ciki a wannan shekara a ran 10 ga watan Fabrairu, sakamakon da za a samu a bayan wannan taro zai zama muhimiyar shaidar wannan rahoto.
A cikin mako da ya gabata, a gun taron zartarwa dokoki na jam'iyyar dake rike da mulkin kasar Afrika ta kudu ANC, Zuma ya bayyana cewa, kamata ya yi, gwamnatin ta gabatar da matakai masu amfani domin cimma burin samar da guraben aikin yi miliyan 5 kafin shekarar 2020.(Amina)