in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar hadin gwiwar AU da MDD ta raba kayayyakin jin kai a Dafur
2013-01-22 11:01:16 cri

Sama da tan 456 na kayayyakin amfanin yau da kullum ne aka rabawa al'ummomin a Arewacin Dafur wadanda suka rabu da gidajensu cikin 'yan kwanakin nan, karkashin kulawar tawagar bada tallafin jin kai ta MDD da kungiyar AU, kamar dai yadda mai Magana da yawun MDD Martin Nesirky ya bayyana. A cewar Nesirky daga tsagin MDD, hukumomin 4 ne suka dauki nauyi bada wannan agaji, wanda ya hada da kayayyakin da ba na abinci, ciki har darufa, da kuma na'urorin tace tuwa. Baya ga wannan a cewarsa akwai batun samar da kyakkyawan tsarin gudanarwa, da tsaro ga masu aikin bada agajin, tare da shirin bada tallafi ga rage kaifin yanayin dar-dar dake wanzuwa a yankin Jabel Amir.

Hadin matsi da ake ciki dai a wannan yanki na Arewacin Dafur ya faru ne, bayan da a wannan wata rikiciya barke tsakanin al'ummomin kabilun Abbala da na Beni-Hussein, kan batun mahakar zinari dake yankin na Jabel Amir. Fadan da ya sabbaba mutuwar mutane sama da dari, yayin da wasu 70,000 suka rasa matsugunnansu. Rahotanni daga mahukunta sun tabbatar da cewa fadan kabilancin ya bude kofar gudanar miyagun laifuka, da suka hada da kone wasu kauyuka da wawashe dukiyoyin al'umma, wanda hakan ya janyo karin kwararar 'yan gudun hijira zuwa garuruwan Kabkabiya, da Saraf Omra, da kuma garin Al-sereif.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China