130605_Darfur_Amina
|
Kwamitin kula da ragowar ayyuka na takardar shimfida zaman lafiya a yankin Darfur da aka kulla a birnin Doha ya kira wani kwarya-kwaryar taro a ran 4 ga wata a Doha babban birnin kasar Qatar, inda aka tattauna yadda za'a tabbatar da shirin shimfida zaman lafiya a Darfur.
Wakilan da suka fito daga gwamnatin Sudan da kungiyoyin JEM da LJM masu adawa da gwamnati, da kuma kungiyoyin duniya da na shiyya shiyya, ciki har da kungiyar AU, kungiyar AL, kwamitin sulhu na MDD da dai sauransu sun halarci taron.
A cikin jawabinsa na bude taron, mataimakin firaministan kasar Qatar kuma ministan mai kula da harkokin ciki gida na kasar Ahmed Abdullah Al Mohamoud ya yi kira ga wasu kungiyoyin adawa da gwamnati da ba su shiga shawarwarin ba da su dauki nauyin dake wuyansu na tabbatar da zaman lafiya a yankin,
kuma yana fatan za a samu tabbacin sulhuntawa tsakanin su a dukan fannoni cikin sauri a Darfur, ya ce,
"Ya kamata, kasashen duniya su yi iyakacin kokari ta yadda za a tabbatar da tsagaita bude wuta da samun sulhuntawa a Darfur cikin sauri bisa ka'idojin dake cikin takardar shimfida zaman lafiya a Darfur da aka kulla a Doha."
An ce, a watan Mayu na shekarar 2011, a karkashin shawarar kasar Qatar, masu ruwa da tsaki a Darfur sun gabatar da wannan takardar shimfida zaman lafiya a Darfur da ta shafi fannoni 7, da zummar gaggauta shimfida zaman lafiya a yankin. Sai dai, a ran 12 ga watan Mayu da ya gabata, an kai hari ga shugaban kungiyar JEM Muhammad Bashir Ahmed inda aka hallaka shi, kungiyar da ta sa hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin kasar Sudan, abin da ya kawo illa sosai ga halin siyasa da tsaro da Darfur ke ciki. A gane da al'amarinAhmed Abdullah Al Mohamoud ya ce:
"An kira wannan taro da zummar samarwa kasashen duniya da bangarorin da rikicin ya shafa wani sako cewa, daukar matakin siyasa hanya daya tilo ce wajen waware rikicin. Ya kamata bangarorin daban-daban su aiwatar da yarjejeniyar da aka kulla a gaba wajen shimfida zaman lafiya. Kasashen duniya kuwa za su saka takunkumi mai tsakani kan wadanda suka aikata ayyuka nuna karfin tuwo."
Bayan jawabinsa, an yi taro a asirce. A hakika dai, kafin an yi wannan taro a ran 3 ga wata, Ahmed Abdullah Al Mahamoud ya gana da shugaban hukumar madafun iko ta yankin Darfur kuma shugaban kungiyar LJM Tijani Cisse da wakilan gwamnatin kasar Sudan da na AU. Bangarori daban-daban sun waiwayi yadda aka raya da farfado da yankin Darfur, sa'i daya kuma, sun yi Allah wadai da kisan gillar da aka yiwa wasu shugabannin da suka sa hannu kan yarjejeniyar shimfida zaman lafiya.
Yankin Darfur yana dai yammacin kasar Sudan ne, wanda yake iyaka da kasashen Libya, Chadi da Afrika ta tsakiya. Tun daga shekarar 2003, wasu kungiyoyin masu dauke da makamai a wurin suke tada zaune tsaye bisa dalilin cewa, gwamnatin na nuna halin ko in kula kan wannan yanki. Bisa kokarin da kasar Qatar da sauran kungiyoyin duniya suke yi, wasu kungiyoyi masu dauke da makamai a yankin sun cimma sulhu da gwamnatin kasar daga shekarar 2011, amma duk da haka, har yanzu akwai wasu kungiyoyi da suke kin yarda da tsagaita bude wuta. (Amina)