Karamin magatakardan MDD a fuskar ayyukan kafa zaman lafiya Herve Ladsous ya yi Allah wadai da harin da aka kaiwa jami'an aikin kafa zaman lafiya na hadin gwiwa tsakanin kungiyar hada kan kasashen Afirka da MDD a Darfur (UNAMID), inda ya baiyana cewa kaiwa ma'ikatan kafa zaman lafiya hari laifi ne, in ji karamin mai magana da yawun MDD, Farhan Haq, yayin da yake jawabi ga 'yan jarida.
An ji wa ma'aikatan kafa zaman lafiya guda 3 rauni lokacin da wasu da ba'a san ko su waye ba suka yi wa tawagar sintiri ta dakarun MDD kwanton bauna a kusa da Labado dake gabashin Darfur, in ji hukumar.
Ladsous wanda bai jima da kamala rangadin kwanaki 3 a Sudan din ba ya ce, wajibi a cafko a kuma hukunta wadanda suka kai wannan hari. (Lami Ali)