in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Magatakardar MDD ya yi Allah wadai da kisan jami'an wanzar da zaman lafiya da ke Darfur
2013-07-14 16:13:17 cri
Rahotanni daga ofishin babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon sun rawaito shi na Allah wadai da kisan wasu jami'an aikin wanzar da zaman lafiya na MDD 'yan asalin kasar Tanzania su 7 a kudancin Darfur na kasar Sudan.

Cikin wata sanarwar da kakakinsa ya fita, Mr. Ban ya bayyana wannan lamari da cewa wani mummunan aikin rashin tausayi ne. Sanarwar ta bayyana cewa, wadannan jami'ai da wasu mahara da kawo yanzu ba a tantance da su ba, an yi musu kwantan bauna ne a Khor Abeche dake Kudancin yankin Darfur, inda baya ga mutane 7 da suka hallaka, wasu karin 17 suka samu munanan raunuka, ciki hadda jami'an 'yan sandan tawagar MDD ta UNAMID 4.

Wannan ne dai hari na 3 cikin makwanni 3 da aka kai kan tawagar ma'aikatan wanzar da zaman lafiya dake kasar ta Sudan, don haka magatakardar MDDr ya yi kira ga mahukuntan kasar da su hanzarta daukar matakan hukunta wadanda ke da hannu cikin faruwar wannan ta'asa. Tun dai cikin shekarar 2008, lokacin da aka fara jibge dakarun tawagar ta UNAMID, ake kai hare-hare kan ma'aikatanta, lamarin da kawo yanzu ya sabbaba kisan jami'ai kimanin 40. Kawo wannan lakaci dai tawagar na da sojoji sama da 19,550 da kuma 'yan sanda 6,400 a kasar ta Sudan. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China