in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin kasar Sudan sun yi musayar wuta tare da dakaru masu adawa da gwamnatin kasar a yankin Darfur
2012-06-03 20:04:14 cri
Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Sudan suka bayar a ranar 3 ga wannan wata, an ce, sojojin kasar da dakaru masu adawa wato kungiyar JEM sun yi rikici a yankin Darfur dake yammacin kasar a ranar 2 ga wannan wata, wanda ya haddasa mutuwa da raunatar wasu mutane daga bangarorin biyu.

Labarin ya tsamo maganar kakakin sojojin kasar Sudan na cewa, a ranar 2 ga wannan wata da yamma, sojojin kasar sun murkushe harin da dakarun kungiyar JEM suka kai a yankin Fataha dake da kimanin kilomita 600 da kudu da babban birnin jihar Darfur ta arewa, sojojin sun harbe dakaru 45 har lahira tare da lalata motocinsu 16. Saidai ba a bayyana daga bangaren sojojin kasar ko mutane nawa suka mutu ko jin rauni sakamakon wannan rikici.

Kakakin JEM ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, membobin kungiyarsa sun kai hari ga wani sansanin sojojin kasar Sudan dake yankin Fataha. Sun harbe sojojin kasar da dama har lahira tare da lalata motoci fiye da 10.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China