Ya zuwa yanzu, kwanaki 16 ke nan, bayan abkuwar bala'in girgizar kasar da karfinsa ya kai maki 7 a gundumar Lushan da ke lardin Sichuan a kasar Sin a ranar 20 ga watan da ya gabata, kuma an samu wasu matsalolin da ya shafi raban kayayyakin agaji, da tsugunar da jama'ar da suke fama da bala'in, sannan da sake yin gine-gine, amma duk da hakan, gwamnatin birnin Ya'an ta tashi tsaye don biyan bukatun jama'a, da inganta aikin kiyaye jama'a, da warware matsaloli da ya shafe su.
Dangane da hakan. Bisa labarin da hukumar kiwon lafiya ta birnin Ya'an ta bayar, an ce, ba a samu barkewar annoba sakamakon bala'in girgizar kasar ba. Ganin haka, yanzu, birnin Ya'an yana gudanar da ayyukan tsabtacce muhalli, da sa ido game da ruwan sha, da yaki da annoba a wuraren da ake tsugunar da jama'a.(Bako)