An farfado da yanayin zaman rayuwar al'umma a yankunan da bala'in girgizar kasa na Lushan ya ritsa da su a kasar Sin
Ranar 20 ga wata, rana ce ta cika wata guda cif da aukuwar bala'in girgizar kasar da ya fada wa gundumar Lushan da ke lardin Sichuan a kasar Sin. Bisa sabuwar kididdigar da hedkwatar ba da umurni game da yaki da bala'i da ceton jama'a ta lardin Sichuan ta kasar Sin ta bayar, an ce, yanzu, an riga an tsugunar da jama'a sama da dubu 790, da ke fama da bala'in, kuma kashi 80 cikin 100 na wadanda suka jikkata sun riga sun samu waraka, kuma an farfado da yanayin zaman rayuwar al'umma a wuraren da bala'in ya shafa, tare da gaggauta gudanar da aikin rigakafin hadarurruka dake iya aukuwa bayan girgizar kasar.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, yanzu haka an sake bude kashi 70 cikin 100 na shagunan dake wuraren da bala'in ya ritsa da su, kuma sama da rabin masana'antun da suka daina aiki sakamakon bala'in sun farfado.
Ban da wannan kuma, yanzu, mutane sama da dubu 15 na gudanar da aikin yaki da bala'i da ceton mutane a wuraren da bala'in ya shafa.(Bako)