in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara taron G8 tare da kaddamar da tattaunawa kan yarjejeniyar cinikayya
2013-06-18 10:31:48 cri

Ana taron kasashe 8 na duniya da suka ci gaba a fuskar masana'antu wato G8 a wajen shakatawa na Lough Erne Resort, inda aka fara da tattauanawa kan yarjejeniyar cinikayya tsakanin tarayyara kasashen Turai (EU) da kuma kasar Amurka.

Yayin taron manema labarai na hadin gwiwa, firaministan Burtaniya David Cameron yayin jawabinsa tare da shugaban majalisar gudanar da kungiyar EU Herman Van Rompuy, shugaban hukumar EU Jose Manuel Barroso da kuma shugaban kasar Amurka Barack Obama, ya bayyana cewa, suna tattauanawa kan batun da aka iya zama wata babbar yarjejeniyar cinikayya da aka taba kullawa a tarihin duniya.

Shugaba Obama ya bayyana cewa, hadin gwiwa a fuskar cinikayya da zuba jari na da muhimmanci ga tattalin arziki, kuma gwamnatinsa za ta dora muhimmanci a kai.

Kasar Amurka da kasashen Turai ne ke da dangantakar tattalin arziki mafi girma a duniya, inda ya kai rabin hada hadar tattalin arzikin duniya baki daya, kuma kashi 30 cikin dari na cinikayya a duniya. Wannan yarjejeniya tsakanin bangarorin biyu za ta yi kokarin kawar da dukkan wani haraji kan cinikayya, kana za ta samar da yanki mafi girma na yin cinikayya babu haraji a fadin duniya.

Daga cikin shugabanni dake halartar wannan taro, akwai shugaba Obama, firaministan Italiya Enrico Letta, firaministan kasar Canada Stephen Harper, firaministan kasar Japan Shinzo Abe, shugaban kasar Faransa Francois Hollande, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da shugabar kasar Jamus Angela Merkel da kuma Barroso.

Baya ga batun rikicin kasar Sirya, taron na kwanaki biyu zai mai da hankali kan batun tattalin arziki da kuma na haraji. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China