in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Zimbabwe ya sanar da lokacin yin babban zabe
2013-06-14 14:59:08 cri

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya sanar a ran 13 ga wata cewa, za a gudanar da babban zabe na kasar a ran 31 ga watan Yuli, amma firaministan kasar Morgan Tsvangirai bai amince da hakan ba.

Mugabe ya ba da sanarwar a wannan rana cewa, ya riga ya yi amfani da ikonsa na shugaba wajen gyara dokar zabe, kuma zai gabatar da sassan daftarin dokar da ya gyara ga jama'a, saboda a fadinsa babu isashen lokacin jiran majalisa da ta zartas da daftarin. An fara yin rajistar masu kada kuri'a a wannan mako.

A kuma wannan rana, babban wanda ke takara da Mugabe, kuma firaministan gwamnatin hadin gwiwa Morgan Tsvangirai ya nuna cewa, gudanar da zabe cikin kwanaki 45 bai dace ba saboda babu isashen lokaci. Zai nuna rashin jin dadin nasa a gaban kotu tare da neman bukatar a daidaita lokacin yin zabe. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China