Za a gudanar da babban zaben shugaba, na 'yan majalisar dokoki da kuma na kananan hukumomi yankunan kasar a ran 31 ga watan da muke ciki a kasar Zimbabwe. Shugaba mai ci mista robert Mugabe mai shekaru 89 zai halarci babban zaben inda zai fafata tare da faraninstan kasar na yanzu kuma shugaban jam'iyyar adawa ta kasar mista Morgan Tsvangirai. Koda yake a halin yanzu, ba a samu isassun kudaden gudanar da zabubbukan ba, haka kuma ba'a da tabbas kan ainahin yawan adadin mutanen da suka yi rajista ba, lamarin da ya janyo damuwar gamayyar kasa da kasa kan wadannan zabubbuka na kasar Zimbabwe.
Kungiyar raya kudancin kasashen Afirka SADC da kungiyar tarayyar kasashen Afirka AU suka aike da masu sa ido sama da 500 domin sanin halin da ake ciki a wuraren jefa kuri'u guda 210. Bugu da kari, kwamitin kula da harkokin babban zaben kasar Zimbabwe ya bayyana cewa, za a fitar da sakamakon babban zabe kwanaki 5 bayan jefa kuri'un. (Maryam)