in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Abokan hamayyar siyasa a Zimbabwe sun amince su nemi kotu ta jinkirta lokacin zabe
2013-06-20 10:22:01 cri

A ranar Laraba, shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe da babban abokin hamayyarsa na siyasa a gwamnatin hadaka suka amince su shigar da bukata ga kotun dokokin kasar domin neman a kara wa'adin lokaci da za'a gudanar da zabe, wato nan gaba da 31 ga watan Yulin shekarar nan ke nan.

Wannan yarjejeniya dai ta biyo bayan shawara da kungiyar bunkasa al'ummar kudancin Afirka (SADC) ta bayar a karshen makon da ya wuce, inda ta bukaci gwamnatin hadakar ta je kotu domin neman a daga lokacin zabe wanda shugaba Mugabe shi kadai ya tsayar a makon da ya wuce.

Shugabannin uku, wato Mugabe, firaminista Morgan Tsvangirai, da ministan kasuwanci da masana'antu Welshman Ncube sun gana a gidan gwamnati ranar Laraba, suka kuma amince kan hakan, in ji mai magana da yawun Tsvangirai, Luke Tambirinyoka yayin bayani ga kamfanin dillancin labaran kasar Sin, Xinhua.

Ana ganin cewa, shugaba Mugabe da firaminista Morgan Tsvangirai su ne manyan 'yan takarar kujerar shugabancin kasar a zaben.

An gabatar da taron kungiyar SADC na musamman a karshen makon da ya wuce a Maputo, babban birnin kasar Mozanbique inda ta ba da shawara ga gwamnatin Zimbabwe da ta nemi kotun ta daga ranar zabe wato 31 ga Yuli.

Yayin da shugaba Mugabe ke son a yi zabe da wuri, Tsvangirai da Ncube su kuma son suke yi a gabatar da sauyi a fannonin siyasa, kafofin labarai da na tsaro kafin lokacin da za'a yi zabe da zai kawo karshen gwamnatin hadakar.

To amma dai kotun ita ce ke da wuka da nama game da ko za'a daga lokacin zaben ko a'a, bayan an gabatar da wannan bukata gare ta. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China