Wannan dai bukata ta biyo bayan wani taron tattaunawa na musamman da jagororin suka gudanar karkashin inuwar kungiyar SADC a birnin Maputo. Da yake gabatar da wannan bukata, babban sakataren kungiyar ta SADC Tomaz Salomao ya ce, akwai bukatar neman kotun kasar ta Zimbabwe mai lura da tanaje-tanajen kundin mulki, ta sauya lokacin zaben daga ranar 31 ga watan na Yuli zuwa wani lokaci a nan gaba.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai shugaba Robert Mugabe ya sanar da wannan rana, a matsayin ranar da za a gudanar da zabukan shugaban kasar, da na 'yan majalisu, da kuma na kananan hukumomin kasar, ko da yake dai tsohon dan hamayyar shugaban kasar, kuma firaministan kasar Morgan Tsvangirai ya nuna rashin amincewarsa da wannan mataki. Tsvangirai ya ce, akwai bukatar samun isasshen lokacin warware wasu muhimman batutuwa, ciki hadda harkar tsaro kafin gudanar da zabukan.(Saminu)