in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babbar kotun Zimbabwe ta dage sauraron kara kan batun sanya ranar babban zaben kasar
2013-06-27 10:29:53 cri

A ranar Labara 26 ga watan nan ne, babbar kotun kasar Zimbabwe ta dage zaman sauraron karar da aka shigar gabanta, don gane da batun sanya ranar gudanar babban zaben kasar, lamarin da tuni ya jima yana yamutsa hazo a fagen siyasa, musamman tsakanin manyan jam'iyyun siyasar kasar.

Tuni dai shugaban kasar Robert Mugabe ya ayyana ranar 28 ga wata Yunin nan a matsayin ranar fidda 'yan takara, yayin da kuma ranar 31 ga watan Yuli mai zuwa za ta zamo ranar da za a kada kuri'un babban zaben.

Sai dai manyan 'yan adawarsa, firaministan kasar Morgan Tsvangirai da Ncube, sun yi watsi da wannan batu, tare da mika kokensu ga kungiyar bunkasa yankin kudancin Afirka ta SADC. Hakan kuma ya sanya SADC umartar ministan shari'ar kasar Patrick Chinamasa, da ya gabatar wa wancan kotu bukatar kara wa'adin gudanar zaben da makonni biyu.

Da yake bayyana dage sauraron shari'ar, mai shari'a Godfrey Chidyausiku ya ce, kotun za ta bai wa sabbin kararraki biyu da Tsvangirai da Ncube suka shigar muhimmanci, tare da zama tare da dukkanin jam'iyyun da abin ya shafa, kafin sanya ranar ci gaba da sauraron karar.

Su dai sabbin kararrakin da manyan 'yan adawar suka gabatar, na bukatar kotun ta umarci kotu mai kula da harkokin da suka shafi kundin mulkin kasar, sauya matsayinta kan kudurin gudanar da zabe kafin ranar 31 ga watan Yulin wannan shekara da muke ciki. Har ila yau, 'yan adawar na son kotun ta soke ranar gudanar zaben da tuni shugaban kasar ya ayyana.

A wani ci gaban kuma kotun dake lura da batun fidda 'yan takara a kasar ta Zimbabwe, za ta yi zaman karbar sunayen 'yan takara da na kwararru ta fuskar shari'a a ranar Juma'a 28 ga watan nan, aikin da ta ce ba shi da wata nasaba da batun dage ranar sauraron kara kan gudanar babban zaben kasar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China