in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu sa ido na AU sun gana da firaministan Zimbabwe game da zaben kasar
2013-06-26 10:42:12 cri

A ranar Talata ne firaministan Zimbabwe Morgan Tsvangirai, ya gana da tawagar masu sa ido na kungiyar AU da suka zo kasar don duba yanayin siyasar kasar.

Kakakin Tsvangirai, Luke Tamborinyoka, ya bayyana cewa, firaministan ya yi wa tawagar mai wakilai uku bayani game da ci gaban da aka samu game da siyasa a kasar, ciki har da batutuwan da suka shafi hukuncin da kotun kundin tsarin mulkin kasar ta yanke da shirin rajistar masu zabe da ke gudanarwa.

Ita dai tawagar 'yan kallon, wani bangare ne na tawagar masu sa ido na kungiyar AU mai wakilai 9 da suka iso kasar gabanin zabukan kasar da ake ganin Mugabe da Tsvangirai ne za su kasance manyan 'yan takarar mukamin shugabancin kasar.

Tun a shekarar 2009 ne mutanen biyu suka kafa gwamnatin hadaka, lokacin da kungiyar SADC ta shiga tsakani na ganin an raba madafun iko, sakamakon tashin hankali da rigingimun siyasar da suka faru a shekarar 2008.

A kwanakin nan ne kotun kundin tsarin mulkin kasar ta Zimbabwe, ta yanke hukuncin cewa, wajibi ne a gudanar da zabe a ranar 31 ga watan Yulin, abin da ya sa shugaba Mugabe ya tsayar da wannan rana a matsayin ranar da za a yi zabukan kasar.

Ko da yake abokan adawarsa a gwamnatin hadaka wato Tsvangarai da kuma ministan kasuwanci da masana'antu Welshman Ncube, sun ki amincewa da wannan rana, inda suka bukaci kungiyar SADC a yayin taron kolin na musamman da aka yi a Maputo, babban birnin Mozambique, da a canja ranar, ta yadda za a aiwatar da gyare-gyaren da suka dace don gudanar da zabe cikin adalci

A nata bayanin, kungiyar SADC, ta bukaci gwamnatin Zimbabwe, da ta canja ranar zaben, kana ta nemi ministan shari'a da harkokin doka na kasar Patrick Chinamasa, da ya gabatar da roko a kotun kundin tsarin mulkin kasar na neman karin lokacin zabukan kasar da a baya aka shirya gudanarwa a ranar 31 ga watan Yuli. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China