Rahotannin baya bayan nan daga Zimbabwe na nuna cewa, jam'iyyar firaminista Morgan Tsvangirai ta MDC ta shiga wani kawance da jam'iyyun MKD da Zanu-Ndonga, a yunkurin da jam'iyyun adawar kasar ke yi na kalubalantar jam'iyyar shugaba Mugabe da ke mulkin kasar a halin yanzu.
Firaministan kasar ta Zimbabwe kuma tsohon 'dan adawar shugaba Mugabe dai zai kasance cikin jerin masu burin ganin shugaban kasar ya bar kujerar mulki bayan kammalar babban zaben kasar dake tafe nan da 'dan lokaci, a kuma wannan karo ya samu goyon bayan wani tsohon na hannun damar Mugaba wato Mavambo Kusile Dawn na jam'iyyar MKD, da kuma jagorar jam'iyyar Zanu-Ndonga Reketai Semwayo.
A nan dai sa ran kada kuri'un babban zaben kasar dake tafe ne a ranar 31 ga watan nan na Yuli, inda al'ummar Zimbabwe za su zabi sabon shugaban kasa, da mambobin majalissar dokokin kasar sama da 200, da kuma mambobin majalissar zartaswar kananan hukumomi kimanin 2,000.
Cikin manyan 'yan takarar kujerar shugabancin kasar, akwai shugaban Mugabe dake kan karagar mulki a yanzu haka, da kuma firaminsta Tsvangarai, 'yan takarar da tuni suka kaddamar da yakin neman zabe, tare da manufofinsu ga al'ummar kasar. (Saminu)