Bisa labarin da aka bayar, an ce, zuwa ranar Litinin 29 ga wata, a cikin wadanda suka jikkata a sakamakon abkuwar bala'in, mutane 44 ne suke cikin mawuyacin hali, yayin da wasu 49 suka ji rauni sosai sai dai dukkansu suna samun jiyya a asibitin Huaxi da na lardin Sichuan da kuma babban asibitin yankin soja na Chengdu.
Bayan da aka fara farfado da gundumar Lushan da bala'in girgizar kasa ya shafe ta, an kusan daidaita batun ciyarwa, da wurin kwana, da kuma amfani da wutar lantarki da ruwan sha na jama'a, amma gyaran na'urori, yin aski, samun jiyya da sauransu su ne suka fi damun mutanen. A cikin jerin kwanakin da suka gabata, rukunin ba da hidimomi na rundunar sojan dake Chengdu ya shiga kauyuka domin ba da hidima, tare da taimakawa mutane wajen daidaita matsalolin da suke fuskanta a rayuwa.(Fatima)