Luxemburgo mai shekaru 61 da haihuwa, wanda a baya ya taba horas da 'yan wasan kasar Brazil, ya shiga tsaka mai wuya ne dai tun lokacin da kulaf dinsa ya sha kashi a hannun kulaf din Independiente Santa Fe na Colombia a gasar cin kofin Libertadores da aka buga cikin watan da ya gabata.
Da yake karin haske don gane da wannan batu a ranar Asabar din data gabata, manajan kulaf din na Gremio Rui Costa, cewa yayi lokaci yayi da za a dauki matakin daidaita al'amura a wannan kulaf, tun kafin al'amura su karasa lalacewa, ciki kuwa hadda shawarar da aka yanke ta sallamar kocin na yanzu.
Yayinda koci Luxemburgo ke sallama da kulaf din na Gremio, masu horas da 'yan wasa kamarsu Celso Roth, da Renato Gaucho, da Muricy Remalho, na cikin wadanda ake zaton za a maye gurbinsa da daya daga cikinsu. Kulaf din na Gremio dai shine na 7 a jadawalin kulaflikan dake ajin kwararrun kasar ta Brazil, inda yake da maki 8 cikin wasanni 5 da ya riga ya buga. (Saminu)