in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Neymar Ya Ce Babu Wata Matsala Game Da Batun Taka Leda A Sabon Kulaf Dinsa
2013-07-05 15:55:27 cri

Dan wasan kasar Brazil din nan da a yanzu tauraronsa ke haskakawa a fagen murza leda wato Neymar da Silva Santos, ya bayyana kyakkyawan fatansa ga batun komawarsa kulaf din Barcelona dake kasar Sifaniya, yana mai cewa babu wata matsala da zata hana shi taka leda yadda ya kamata tare da sauran takwarorinsa a Bercalonan.

Neymar ya yi wannan tsokaci ne bayan kulaf dinsa na kasar Barazil ya samu nasarar lallasa takwaransa na kasar Sifaniya da 3 da nema, a karshen gasar cin kofin zakarun nahiyoyi da aka buga ranar Lahadin data gabata. A kwai 'yan wasa 6 dake kulaf din kasar ta Sifaniya, wadanda nan da 'yan kwanaki Neymar zai fara taka leda tare da su a Bercelona, don gane da hakan wannan dan wasa ya ce dama kwallo kafa haka ta gada, babu abinda zai hasa su sake hadewa a sabon kulaf din nasa, su kuma taka leda tare, duk kuwa da cewa idan yana bugawa kulaf din kasarsa kwallo, to fa ba sani-ba-sabo. Mai tsaron bayan Sifaniya Gerard Pique na cikin wadannan 'yan wasa da Neymar ya kara da su, inda yayin fafatawar da suka yi a wasan na karshe, alkalin wasa ya sallami Pique, bayanda ya tabbatar cewa ya yiwa Neymar keta.

Don gane da batun nasarar da ya samu ta karbar lambar girmamawa, ta dan wasa mafi hazaka a gasar cin kofin zakarun nahiyoyin kuwa, Neymar wanda ya jefa kwallaye 4 a zare cikin wasanni 5 da ya buga, yace hakan nasara ce babba gareshi, kasancewar ya dade yana ganin kimar wadanda suka samu wannan nasara a baya. Har ila yau dan wasan ya bayyana farin ciki kan nasarar da kasarsa ta samu a wannan gasa, yana mai cewa sun yi dukkanin abinda ya dace ko wane shahararren kulaf ya yi.

A wani ci gaban kuma an ce za a yiwa Neymar wata karamar fida a makogwaronsa, a ranar Juma'ar nan mai zuwa kafin tashinsa zuwa Sifaniya, don gane da hakan dan wasan yace ya dade yana fama da ciwo a makoshin nasa, don haka aka yanke shawarar yi masa aiki domin dai magance matsalar baki daya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China