Ga dukkanin wanda ke kallon wasannin kwallon kafa daga nesa, na iya zaton cewa nahiyar turai ce kadai ke karbar bakuncin 'yan wasa daga nahiyar Afirka, wadanda ke zuwa domin taka leda a manyan kulaflikan ajin kwararru dake wannan nahiya. Sai dai wasu rahotanni da ke fitowa daga kasar Nepal a baya-bayan nan, na nuna cewa abin ba haka yake ba, domin kuwa zancen nan da ake yi kafofin watsa labarun kasar ta Nepal na cewa, 'yan wasa dake da nufin sake samun damar kwarewa, na kwarara cikin kasar musamman ma daga nahiyar ta Afirka a kowane lokaci.
Da yawa-yawan mutane musamman wadanda ke duban kasashen duniya ta fuskar abinda ido ka iya hanga, abinda yafi jan hankali don gane da wannan kasa shi ne, irin abubuwan da 'yan yawon shakatawa ke harin zuwa gani, ciki hadda babban dutsen nan na Himalaya, da kuma Dutse Qomolangma wanda aka fi sani da "mount Everest", wuraren da suka kasance, manyan burin masu son hawa manyan duwatsu dake sararin wannan duniya. Sai dai wannan buri wata kila ba shi ne na dubban matasa dake halartar wannan kasa daga nahiyar Afirka ba, Domin kuwa a cewar hukumar lura da wasan kwallon kafa ta kasar Nepal, gasar kwallon kafa ta ajin kwararru ta kasar, na matukar janyo hankalin matsan 'yan wasa daga Afirka, wadanda ke fatan sanya sunayen su a kundin tarihin kwallon kafar nahiyar Asiya, musamman a kasahen India da kuma Kudu maso Gabashin nahiyar ta Asiya.
Wancan rahoto yace a dukkanin shekara, wannan gasa ta kakar wasanni da akan gudanar cikin watanni 3, na sanya matasan 'yan kwallo garzayawa kasar ta Nepal, wasunsu dauke da takardar kwantiragin taka leda a kulaflikan da ke shiga gasar, yayin da wasu ke zuwa domin neman gurbi a wasu kulaflika, lamarin da kan kaisu ga shiga takara da sauran masu neman shiga a dama dasu.
Wani matashi da shekaru 19 da haihuwa daga Nijeriya mai suna Adewumi Femi Joshua, wanda ke bugawa shahararren kulaf din dake rike da kambin gasar ajin kwararru a kasar ta Nepal mai suna "Three Star", ya bayyanawa kamfanin dillancin labarum kasar Sin Xinhua cewa, batun shiga a dama da su a wannan kasa ta fuskar kwallon kafa ba wai batu ne na neman kudi kawai ba. Joshua ya ce shi kam yaje wannan kasa ne saboda wani dalili na daban.
"Ban taba jin labarin wannan kasa ba, har sai lokacin da yaya na dake aiki a matsayin mai horas da 'yan wasa a India ya shawarce ni da zuwa Nepal dake makwaftaka da Indian, domin na gwada sa'a ta, idan hali ya yi, in share fagen bunkasa sana'ar kwallon kafa ta a wannan nahiya ta Asiya. Wannan yaya nawa ya fada min cewa akwai 'yan wasa kwararru a wannan kasa, kuma tabbas idan naje, zan sake samun gogewa, hakan kuwa aka yi" a kalaman matashi Joshua.
A wasu lokuta ba wai kawai su 'yan wasan daga kasahen Afirka ne ke son zuwa wannan kasa ba, wani jikon, su kansu kulaflikan ne ke zuwa Afirka domin gayyato 'yan wasan. Hakan kuwa baya rasa nasaba da arahar 'yan wasan na Afirka, wadanda a cewar shugaban hukumar wasannin kasar ta Nepal Indra Man Tuladhar, sun fi 'yan wasan gida araha, da saukin dauka. Bugu da kari Tuladhar yace wani sauki ma ga daukar 'yan wasa daga Afirka shine, suna iya sanya hannu kan kwantiragin watannin Uku, maimakon 'yan wasan gida, da a mafi yawan lokaci ke bukatar kwangilar shekara guda. Har wa yau akwai batun karfin jiki da 'yan Afirkan suka dara 'yan wasan kasar. Sa'an nan 'yan Afirka dake taka leda a Nepal din sun dade da kafa tarihin aiki tukuru, sama da takwarorinsu na gida.
A halin da ake ciki ma dai Tuladhar wanda kuma ke jagorantar daya daga manyan kulaflikan kasar 14, na fatan daukar 'yan wasa 4 daga Afirka a kakar wasa ta bana. Kamar dai yadda dokar hukumar kwallon kafar kasar ta tanaji cewa babu wani kulaf da aka yarjewa daukar bakin 'yan wasa daga waje da yawansu ya zarta 4.
Cikin 'yan wasan nahiyar Afirka da suke taka leda a wannan kasa akwai wani matashi mai suna Ziakhi Lenoce Dodoz daga kasar Ivory Coast, wanda sabanin Joshua, labarin zuwansa wannan kasa ba mai dadi bane. A cewar Dodoz wani tsohon dan wasan kasar Camaro ne ya yi masa romon baka, cewa zai samu makudan kudade idan har ya je wannan kasa domin taka leda. Amma a cewar sa "da sauka ta filin jirgin wannan kasa na lura da da irin gine-ginen dake ciki, na tabbatar da cewa Nepal ba kasace mai arziki, da har mutum zai samu wasu kudade da yawa ba". Duk da haka yace a yanzu haka baya nadamar zuwa wannan kasa, duk da cewa abinda yake samu bai wuce dalar Amurka 1,300 a kowane wata ba, domin kuwa yace ya samu jin dadi da annashuwa, da mutane masu san baki, wadanda a koda yaushe ke burin tattaunawa da shi.
Wani jawabi da ya rubuta kan shafin sa na yanar gizo ya bayyana yadda da farkon zuwansa kasar ta Nepal ya rika jin kewar gida, ya kan kuma ji haushi idan mutane sun kira shi da Kalmar "Hapsi" dake nufin bakar fata a yaren kasar. Amma daga baya Dodoz yace ya fahimci wannan kalma bata nufin wani abu, illa dai fayyace launin sa daga na sauran al'ummar dake fararen fata.
A karshe dai wannan matashin dan kwallo ya yaba tsarin gudanar wasan kwallo a wannan kasa ta Nepal, da ma irin kwazon 'yan wasan kasar, wadanda ya ce haduwa da su, ya taimaka masa wajen karfafa basirarsa a wannan fage, koda yake dai yace gwamnatin kasar bata iya samar da isassun kudade domin bunkasa wannan fanni na kwallon kafa.(Saminu Alhassan)