A farkon watan Nuwanba na bana, hukumar ta gabatar da jerin sunayen 'yan wasa 10 da suka shiga takarar lashe wannan lambar yabo. Guda biyar cikinsu sun samu damar shiga zagayen karshe na takarar. Da farko ana ganin cewa, mashahuran 'yan wasa irinsu Didier Yves Drogba da George Boateng sun fi samun damar lashe wannan lambar yabo. Amma a wasu gasannin da ya shiga Drogba bai nuna kwarewa sosai ba watakila domin shekarunsa sun karu, saboda haka, a cikin jerin sunayen 'yan wasa 5 na karshe hukumar wasan kwallon kafa ta Afirka ta zabi Yaya Touré a matsayin wakilin 'yan wasan kasar Cote d'Ivoire.
Ban da haka kuma, duk da cewa Boateng ya taka rawar gani a gasannin da aka gudanar a shekaru 2 da suka wuce, amma ya sanar da janyewa daga kungiyar kasar Ghana a kwanakin baya, wannan ya zama dalilin da ya sa sunansa bai fito ba a jerin sunayen. Don haka, a jerin sunayen, ana ganin Eto'o da Yaya Toure sun fi samun damar lashe wannan lambar yabo.