A ranar Alhamis 6 ga wata, wakilin din din din na kasar Sin a MDD Li Baodong ya yi kira ga kasashen duniya da su ba da nasu taimakon wajen ganin an inganta halin da kasar ta Somaliya take ciki domin a samu ci gaba mai armashi.
Mr. Li wanda ke magana a lokacin zama na musamman da kwamitin tsaro na majalissar ta yi game da kasar Somaliya ya ce, kasar Sin tana goyon bayan sabuwar gwamnatin kasar Somaliya a shirinta na shirya kundin tsarin mulki na wucin gadi, aiwatar da tsarin dake kunshe a cikin shawarwari 6, inganta karfin iko, tafiyar da ayyukan gwamnati da kuma wanzar da dokoki a kan dukkan iyakar kasar.
Wakilin din din din a majalaissar har ila yau ya jaddada cewa, tattaunawa ita ce kadai hanyar mafita ga samun zaman lafiyar da ake muradi, yana mai kira ga bangarori daban daban da su dakatar da duk wani tashin hankali su hada hannu domin samar da zaman lafiya a kasar cikin gaggawa, yana mai nuni ga kokarin da kungiyoyin kamar na tarayyar kasashen Afrika AU, da na mulkin kasa da kasa da cigaba, IGAD da sauran kungiyoyin ke yi don ganin hakan ya samu nasara.
Haka kuma Mr. Li ya yi kira da a yi saurin aikawa da ma'aikata na sabuwar ofishin MDD a kan ba da taimako da aka bude a Somaliya tare da kara isasshen kudi ga ofishin ba da kula da ayyukan AU a game da somaliyan AMISOM. (Fatimah)