A ranar Alhamis ne babban jami'in kula da harkokin siyasa na MDD Jeffrey Feltman ya ziyarci kasar Somaliya domin ya jaddada kudurin da majalisar ta yanke na taimakawa gwamnati da al'ummar kasar da ke gabashin Afirka, sakamakon harin da aka kaiwa ofishin MDD da ke Mogadishu a makon da ya gabata.
Mataimakin kakakin MDD Eduardo del Buey, ya shaidawa manema labari cewa, Mr Jeffrey Feltman, mataimakin babban sakataren MDD mai kula da harkokin siyasa ya kuma gana da shugaban Somaliya Sheikh Hassan Mohamud, ma'aikatan diflomasiya da na ma'aikatan MDD da harin na makon da ya gabata ya shafa.
A ranar 19 ga watan Yuni ne, wani harin kunar bakin waken da aka kaiwa ofishin MDD da ke Mogadishu ya yi sanadiyar mutuwar mutane a kalla 15, ciki har da mutane 8 da ke aiki da MDD, harin da kungiyar Al-Shabaab da ke da alaka da al-Qaida ta dauki alhakin kaiwa.
Del Buey ya ce, yayin ziyarar Feltman, an tattauna kan yadda za a samar da matakan tsaro da zaman lafiya ga ma'aikatan MDD da ke aiki a kasar ta Somaliya, inda sabuwar tawagar kula da harkokin siyasa ta MDD ta fara aiki a farkon wannan watan.
Idan ba a manta ba, a ranar 2 ga watan Yuni ne aka kaddamar da tawagar MDD da za ta taimakawa Somaliya (UNSOM) wadda aka dorawa nauyin samar da kwarewa a bangarorin da suka kama daga shirin tafiyar da harkokin siyasa zuwa kwance damar makamai, don taimakawa kasar wajen sasantawa, ta yadda za a samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.
A cewar kakakin na MDD, harin da aka kaiwa ofishin majalisar, ba zai sa majalisar ta yi kasa a gwiwa ba a kokarin da take na aiki kafada da kafada da gwamnati da al'ummar kasar ta Somaliya na samarwa kasar ta Somaliya kyakkyawar makoma. (Ibrahim)