Daraktan Kungiyar mai lura da harkokin da suka shafi bunkasa tattalin arziki a karkara da noma Abebe Haile-Gabriel ne ya yi wannan kira, a ranar Asabar 29 ga wata a helkwatar kungiyar ta AU dake birnin Addis Ababa na kasar Habasha, yayin wani taro na share fagen wani babban zama na masu ruwa da tsaki don gane da wannan batu, da ake fatan gudanarwa a ranekun Lahadi da Litinin.
Abebe ya jaddada matsalar rashin isasshen abinci a matsayin wata matsala dake ci gaba da addabar dimbin al'ummar Afirka, wadda kuma a cewarsa za a iya magance ta, muddin dai aka dauki matakan da suka dace. Shi ma a nasa jawabi babban daraktan kungiyar samarda abinci da habaka ayyukan gona ta MDD ko FAO a takaice Jose Graziano Da Silva, cewa ya yi wajibi ne a dauki matakin warware dukkanin dalilai masu alaka da juna, dake habaka wannan matsala ta karancin abinci, a kuma hada karfi da karfi wajen aiki tare, domin dai cimma burin da aka sanya gaba.
Wannan dai taro da kungiyoyin AU, da FAO da cibiyar Lula ta kasar Brazil suka dauki nauyin shiryawa, nada manufar fidda manufofi da tsare-tsare, wadanda za su taimaka ga cimma kudurin magance matsalar yunwa a daukacin nahiyar Afirka, nan da shekara ta 2025 mai zuwa. (Saminu Alhassan)