in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya bayyana damuwa kan halin da ake ciki a kudancin Somaliya
2013-06-14 10:17:51 cri

Kwamitin tsaron MDD ya bayyana rashin jin dadi don gane da halin tabarbarewar yanayin tsaro da ake ciki a yankunan Juba, dake kudancin kasar Somaliya, yana mai kira ga bangarorin da abin ya shafa da su kai zuciya nesa, domin kaucewa daukar matakan da ka iya sake jefa yankunan cikin wani mawuyacin hali.

Cikin wata sanarwa da ta fito daga majalissar, mambobinta sun yi kira da a dauki matakan warware matsalolin dake addabar wannan yanki bisa turbar siyasa. Har ila yau, sanarwar ta bayyana goyon bayan majalissar, don gane da kafa tsarin mulkin Fedaraliyya, da zai hade kan yankunan kasar, ya kuma kawo daidaito a tsakanin sassan jagorancin al'ummarta baki daya.

Daga nan sai sanarwar ta bayyana muhimmacin da ke akwai, don gane da daukar matakan da suka dace kan kungiyar 'yan tada-kayar-bayan nan ta Al-Shabaab, tana mai goyon bayan ayyukan da tawagar kungiyar hadin kan kasashen Afirka dake aikin wanzar da zaman lafiya a Somaliyan AMISOM ke aiwatarwa, musamman a fagen dakile ayyukan masu burin tada zaune-tsaye a kasar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China