Kwamitin tsaron MDD ya yi matukar Allah wadai da harin kunar bakin waken da aka kai wa ofishin MDD dake birnin Mogadishu na kasar Somaliya. An ce, wasu mahara ne dai suka kai wa wannan ofishi hari a ranar Laraba, inda nan take suka hallaka mutane 15, ciki hadda jami'an MDD guda 8. Kuma tuni kungiyar Al-Shabaab mai alaka da Al-Qaida ta ce, ita ce ke da alhakin kai wannan hari.
Cikin wata sanarwa da wakilin din din din na kasar Birtaniya a MDD, kuma shugaban kwamitin tsaron na karba-karba a wannan wata na Yuni Mark Lyall Grant ya fitar, kwamitin ya jaddada aniyarsa ta daukar dukkanin matakan da suka dace wajen ganin an dakile dukkanin nau'o'in ayyukan ta'addanci. Sanarwar ta ce, ayyukan ta'addanci na matukar barazana ga zaman lafiya da tsaron kasashen duniya, kuma irin wadannan laifuka sun cancanci hukunci ga duk wanda ya aikata su, a kowane yanki ne a fannin wannan duniya.
Har ila yau, sanarwar ta jajantawa iyalai da kuma mahukuntan kasar ta Somaliya don gane da faruwar wannan lamari, tare da jan hankalin kasashen duniya da su dauki matakan dakatar da aukuwar ayyukan ta'addanci, su kuma sauke nauyin dake wuyansu, musamman kan al'amuran dake da nasaba da bin dokokin kasa da kasa, da suka shafi kare hakkokin bil'adama da na 'yan gudun hijira.
Bugu da kari, kwamitin tsaron MDD ya jaddada cewa, ayyukan ta'addanci da wasu ke aiwatarwa a Somaliyan ba zai sanyaya gwiwar kwamitin ba, a yukurin da yake yi na taimakawa kasar wajen dawo da yanayin zaman lafiya da daidaito. (Saminu)