Wasu bangarori na 'yan adawar kasar Sham sun bayyana aniyar shiga a dama da su, yayin taron shawarwari don gane da rikicin kasar ta Sham da ake fata gudanarwa, nan gaba a birnin Geneva na kasar Switzerland.
Cikin kungiyoyin da suka nuna sha'awar shiga wannan taron tattaunawa akwai NCB, wadda yayin wani taron manema labarai da jagoranta Hassan Abdul-Azim ya kira a birnin Damascus, ya bayyana cewa, za su dauki dukkanin matakan da suka dace, domin tabbatar da nasarar taron.
Abdul-Azim ya kara da kira ga ragowar kungiyoyin 'yan adawa, da su hada karfi da karfe, wajen ganin sun ba da gudummawarsu ga yunkurin da ake yi na warware matsalar kasar tasu bisa turbar dimokaradiyya.
A farkon watan Afirilun da muke ciki ne dai kasashen Amurka da Rasha, suka amince da sake farfado da shawarwarin da aka soma a bara na birnin Geneva, tare da tabbatar da kudurin kiran babban taron wakilai daga tsagin gwamnati da na 'yan adawar kasar ta Sham. Ana kuma sa ran taron zai mai da hankali ga duba kokarin kasashen biyu, don gane da warware matsalar kasar ta Sham bisa matakan siyasa.
Tuni dai shugaban kasar ta Sham Bashar Al-Assad ya yi maraba da wannan shawara, ko da yake dai ya nuna shakku kan ainihin burin kasashen na yamma don gane da wannan shawara.(Saminu)