Jami'in dai ya yi wannan tsokaci ne biyowa bayan wani sabon fada da ya barke tsakanin dakarun sojin gwamnatin kasar, da kuma 'yan tawayen kungiyar M23, bayan tsagaita wuta na kimanin watanni biyu.
Da yake zantawa da manema labarai, kakakin MDD Martin Nersirky, ya rawaito Moustapha Soumare na bayyana yadda dauki-ba-dadin na baya-bayan nan ya raba dubban mutane da matsugunnansu, matakin da a cewarsa ka iya dagula yanayin ayyukan jin kai a yankin. Daga nan sai Soumare ya yi kira da dukkanin bangarorin da wannan rikici ya shafa, da su dauki matakan tabbatar da kare rayukan fararen hula, kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada.
A wani labarin mai alaka da wannan kuma kimanin mutane 40,000 ne suka tsere zuwa yammacin kasar Uganda, bayan da dakarun rundunar hadakar 'yan adawar kasar ADF suka kaiwa garin Kamango dake Arewacin Kivu hari. (Saminu)