in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta kudu za ta tura dakaraunta DRC
2013-06-22 16:08:45 cri
Mataimakin ministan dangantakar kasa da kasa da hadin gwiwa na Afirka ta kudu Ebrahim Ebrahim ya bayyana ranar Jumma'a cewa Afirka ta kudu za ta tura sojojinta zuwa kasar Jamhuriyar Demokradiyar Congo (DRC) domin shiga sahun aikin kawo zaman lafiya na MDD.

To amma dai Ebrahim bai bayyana ko sojoji nawa ne kasar Afirka ta kudun za ta tura zuwa Jamhuriyar Demokradiyar Congo ba. Afirka ta kudu ta yi alkawarin ba da sojoji sama da 1300 zuwa rundunar mai dakaru 3500.

Ebrahim ya baiyana wa 'yan jarida a Pretoria, yayin jawabi kan abubuwa dake wakana a duniya, cewar sojojin kasar Afirka ta kudu na kan hanyar zuwa Jamhuriyar Demokradiyyar Congo a yanzu.

Ban da kasar Afirka ta kudu, sauran kasashen da suka yi alkawarin ba da sojoji ga rundunar su ne Tanzaniya da Malawi wanda aikinsu shi ne yin gaba da gaba da 'yan tawaye a yankin gabashin kasar DRC.

Ebrahim ya ci gaba da cewa tuni sojojin Tanzaniya suka isa kasar.

A ranar 28 ga watan Maris, kwamitin sulhun MDD ta ba da umarnin tura dakarun shiga tsakani a DRC inda aka damka masu aikin daukar matakin soja kan 'yan tawaye domin a samu dawo da zaman lafiya a yankin gabashin kasar inda ake fama da rikici. (Lami Ali)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China