Bata kashin da aka yi na baya bayan nan a garin Rugari tsakanin kungiyoyi biyu na 'yan tawayen M23 ya janyo babban sauyi kan yanayin tsaro a yankin Arewacin Kivu, in ji Felix Basse, kakakin tawagar sojojin wanzar da zaman lafiya na MDD dake kasar Congo (MONUSCO) a yayin wani taron menama labarai da aka shirya a ranar Laraba a birnin Kinshasa.
A ranar 9 ga watan Maris, a cewar wata majiya mai tushe, dakarun M23 na Bosco Ntaganda sun kai wani hari da misalin karfe bakwai na safe, agogon wurin kan sansanonin Sultani Makenga dake yankin Rugari, in ji kanal Basse tare da bayyana cewa, dole a gaban wannan fito na fito, tawagar MONUSCO ta dauki matakin tura sojojinta daga sansanin soja na Katale da sintiri kan babura har zuwa Rumangabo da Buvunga da zummar kare fararen hula.
Haka kuma mista Basse ya nuna cewa, a ranar 12 da watan Maris na shakarar 2013, yake-yake da manyan makamai sun barke a yankin Rugari, inda aka harba rokoki kimanin 75 zuwa Burambo.
Kusan fararen hula 200 da suka hada maza 131, mata 45 da kananan yara 35 ne suka samu mafaka da kariya kusa da sansanin sojan MDD dake Katale, a yayin da wasu karin fararen hula 200 suka kaura daga Kibumba zuwa birnin Goma tare da rakiyar sojojin MDD dake Katale.
Wannan rikici tsakanin wadannan kungiyoyi biyu na 'yan tawayen M23 ya janyo gudun hijira na mutane 800 a Rumangabo da kuma 500 a Buvunga. (Maman Ada)