Kakakin rundunar sojin kasar ta Uganda Laftana Kanar Paddy Ankunda ne ya tabbatar da daukar wannan mataki, yayin zantawarsa da wakilin kamfanin dillancin labarun kasar Sin Xinhua ta wayar tarho. Rundunar sojin kasar ta Ugandan dai na dari-dari da yiwuwar kwararar mayakan kungiyar ta ADF mai alaka da Al-Qaida, ta hanyar shigarsu ayarin 'yan gudun hijira, daga baya kuma su fara kaddamar da hare-hare a kasar ta Uganda.
A wani ci gaban kuma hukumar MDD mai lura da harkokin 'yan gudun hijira UNHCR ta bayyana cewa, yawan 'yan gudun hijirar dake tururuwa zuwa kasar Uganda daga Congo sun doshi mutum 42,000. A hannu guda ita ma wata kungiyar tallafawa 'yan gudun hijirar mai suna URCS ke nuna halin tsananin bukatar taimako, da 'yan gudun hijirar kasar ta Congo ke ciki a halin yanzu. (Saminu Alhassan)