Wani rahoto da tawagar samar da daidaito ta MDD MONUSCO, dake DRC wato jamhuriyar dimokaradiyyar Congo ya fitar, ya bayyana halin rashin tabbas da yankin arewacin kasar Congo Kinshasa ke ciki.
Mataimakin kakakin MDD Eduardo del Buey ne ya tabbatar da hakan ranar Litinin 4 ga watan nan, yayin taron ganawa da manema labaru na rana da ya gabatar.
A cewarsa, rahoton na MONUSCO na nuni ga matsanancin hali da arewacin Kivu dake gabashin kasar ke ciki a wannan lokaci, yankin da wani bangare na kungiyar M23, da dakarun kungiyar APCLS suka gudanar da hare-hare cikinsa a 'yan kwanakin nan. Hakan a cewar rahoton, kari ne kan ragowar yankuna irin su Kitchanga, inda a ranar Lahadin da ta gabata, wasu dakarun 'yan tawaye suka kai hari kan cibiyar tsaro ta sojojin gwamnatin kasar wato FARDC, suka kuma kame birnin.
Bisa kididdiga, kimanin mutane 80 ne suka rasu, yayin da kuma wasu 100 suka samu raunuka, baya ga wasu 3,000 da suka rasa matsugunansu tun bayan barkewar wannan tashin hankali a yankin na Kitchanga, inda MONUSCO ke da sansaninta.
Bugu da kari a daidai ranar ta Lahadi, dakarun M23 sun sake kutsa kai yankunan Kiwanja da Rutshuru, biyowa bayan janyewar da dakarun gwamnati na FARDC suka yi daga yankunan. Rahoton ya kuma ce, kawo yanzu, jiragen saman yaki masu saukar ungulu na ci gaba da sintiri a yankin Munigi-Kibumba-Kibati.
Tashe-tashen hankula dai da wannan yanki na gabashin Congo Kinshasa yake shan fama da su a 'yan watannin nan, ya sanya mutane da yawansu ya kai dubu 475 rasa matsugunansu, yayin da kuma wasu kimanin dubu 75 suka tsere zuwa makwabtan kasashen Ruwanda da Uganda.(Saminu)