Wanda aka cafke din mai suna Yiblayan Eli, a cewar wata sanarwar da rundunar 'yan sandan ta fitar, na cikin jerin mutane 17 da ake zargi da ta da hargitsi, a garin Lukqun dake gundumar Shanshan ta jihar Xinjiang. Sanarwar ta kara da cewa gungun wadanda ake zargin mabiya ne na wata kungiyar masu tsattsauran ra'ayin addini karkashin jagoransu Ahmatniyaz Sidiq, sun kuma tara kudade, tare da mallakar wukake da fetir, tare da nazartar wurin da suke fatan kaiwa hari tun tsakiyar watan nan na Yuni.
Sanarwar ta kara da cewa sakamakon kame dayansu da 'yan sanda suka yi a ranar Talata 16 ga wata, masu tarzomar sun afkawa ofishin 'yan sandan yankin, da wani ginin hukuma, da wani wuri da ake aikin gini, tare da wasu kantuna biyu, suka kuma cinnawa wasu motocin 'yan sanda guda biyu wuta. An ce cikin mutane da tarzomar ta ritsa da su 16 'yan kabilar Uygur ne. Baya ga mutane 24 da harin na ranar Laraba ya ritsa da su, ciki hadda 'yan sanda biyu, akwai kuma wasu karin mutane 21 da suka jikkata.
'yan sanda sun harbe masu tarzomar 11 a kokarinsu na murkushe tarzomar, suka kuma kame wasu guda 4, yayin da kuma wani guda ya tsere. (Saminu Alhassan)