Dangane da shawarwarin da aka kammala kan batun nukiliya na kasar Iran a birnin Alma-Ata a ran 27 ga wata, Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin tabayyana a ranar 28 ga wata cewa, an samu kyakkyawan sakamako a yayin shawarwarin. Ma iya cewa, an taka mataki na farko wajen kaddamar da tattaunawa kan harkokin da suka shafi batun nukiliya na Iran, haka kuma shawarwarin na taimakawa wajen warware batun nukiliya na Iran
Hua Chunying ta kara da cewa, akwai sauran rina a kaba game da daidaita batun nukiliya na Iran daga dukkan fannoni yadda ya kamata kuma cikin dogon lokaci. Kasar Sin na fatan bangarorin da abin ya shafa za su nuna karfin zuciya da kara nuna sassauci da sahihanci, su kara yin tattaunawa, a kokarin sa kaimi kan warware batun cikin hanzari. Kasar Sin na fatan yin kokari tare da su wajen ci gaba da taka muhimmiyar rawa.