in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu sakamako mai gamsarwa cikin shawarwari kan manyan tsare-tsare da tattalin arziki zagaye na biyar da ke tsakanin Sin da Amurka
2013-07-15 16:28:05 cri
Kwanan baya an rufe shawarwari kan manyan tsare-tsare da tattalin arziki zagaye na biyar da ke tsakanin Sin da Amurka a birnin Washington na kasar Amurka. Ran 12 ga wata, inda aka fidda bayani kan sakamakon da aka samu wajen shawarwarin.

An samar da bayanai guda 91 cikin sakamakon shawarwarin manyan tsare-tsare da suka hada da harkokin hadin gwiwa kan fannoni daban daban da ya shafi makamashi, kiyaye muhalli da dai sauran fannoni guda takwas. Kuma bangarorin 2 sun gane cewa, tuntubar juna tsakanin shugabannin kasashen biyu tana da muhimmanci sosai wajen raya dangantakar kasashen biyu, shi ya sa za su ci gaba da yin tuntubar juna a tsakaninsu.

Kasashen biyu sun kuma sun buga take ga muhimmancin yanayin tsaro na shawarwarin manyan tsare-tsare da kafa kungiyar aiki ta yanar gizo bisa tsarin shawarwarin, inda suka cimma ra'ayi daya kan yin shawarwari kan harkokin intanet.

Kasashen biyu suna son karfafa dangantakar rundunonin sojojin kasashen, kuma sun tsai da kudurin yin zummar kafa tsarin mu'amalar manyan harkokin aikace-aikacen sojojin kasashen.

Sannan kuma za su kara yin tattaunawa kan harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya, za su kuma fara yin hadin gwiwa kan aikace-aikece ta fuskar sauyin yanayi.

Sakamakon da aka samu wajen shawarwarin tattalin arziki sun shafi fannoni hudu:

Na daya, A karfafa manufofin tattalin arziki. Inda Kasashen biyu suka yi alkawarin cewa za su gudanar da harkokin da ya shafi yarjejeniyar G20, da kuma dukufa wajen kaucewar hauhawar farashin kaya.

Sai na biyu, A inganta ayyukan cinikayya da na zuba jari. Kasashen biyu za su dauki matakai da dama wajen zurfafa dangantakar cinikayya da zuba jari da ke tsakaninsu.

Na uku kuma,za'a bunkasa hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa da kuma ka'idojin kasa da kasa. Kasashen biyu sun yi alkawarin cewa za su ci gaba da bunkasa dandalin tattaunawar hadin gwiwar tattalin arzikin kasa da kasa na G20 da kuma gudanar da manufofin yarjejeniyar G20, kuma ba za su amince da ko wane irin kariyar ciniki ba.

Sannan na hudu, A goyi bayan karfafawa da kuma gyare-gyaren sha'anin kudi. Inda Kasashen biyu za su ci gaba da inganta harkokin gyare-gyaren sha'anin kudi cikin kasashen da kuma karfafa ayyukan binciken sha'anin kudin kasashen. Za su kuma gudanar da harkokin sha'anin kudin bisa ka'idojin G20 da kwamitin karfafawar sha'anin kudi da dai sauransu ta yadda za a iya kiyaye karfafawar sha'anin kudin kasa da kasa da kuma kara mu'amalar harkokin sha'anin kudi. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China