A ranar 9 ga wata, agogon wurin, mataimakin firaministan kasar Sin Wang Yang da kuma mamban majalisar gudanarwa ta kasar Yang Jiechi sun yi sharhi a manyan jaridun kasar Amurka, inda suka hango makomar hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da ta Amurka.
A sharhin da ya yi mai taken "karfafa mu'amala don inganta hadin gwiwa" a jaridar "The Wall Street", malam Wang Yang ya nuna cewa, a halin yanzu, Amurka ta fi samun saurin karuwar kayayyakin da take fitarwa zuwa kasashen ketare a kasuwar kasar Sin, a yayin da kasar ta Amurka ta kasance ta biyu cikin abokan cinikayyar kasar Sin.
Hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya da ke tsakanin kasar Sin da kasar Amurka na ci gaba da bunkasa, abin da zai amfana wa jama'ar kasashen biyu, kana zai ba da gudumawa ga farfadowar tattalin arzikin kasa da kasa.
Kulla dangantakar girmama juna da yin hadin gwiwa da kuma cimma moriyar juna tsakanin kasashen biyu, ko shakka babu ya dace da bukatun jama'a da kuma gwamnatocin kasashen biyu, haka kuma buri ne na kasa da kasa.
Shi kuma Yang Jiechi a sharhin da ya yi a jaridar "Washington Post", ya bayyana cewa, hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen biyu na amfana wa jama'arsu. Wannan taro na shawarwari kan manyan tsare-tsare da tattalin arziki da ke tsakanin kasar Sin da kasar Amurka na da muhimmanci sosai, ta fuskar yin musayar ra'ayi tsakanin shugabannin kasashen biyu kan batutuwa masu muhimmanci. Bugu da kari, yayi imani cewa, bisa kokarin bangarorin biyu, za a cimma nasarar taron wanda zai kai ga samun kyawawan sakamako. (Maryam)