Kasar Sin tana fatan bangarori daban daban da batun Syria ya shafa za su tsaya tsayin daka kan manufar warware batun ta hanyar siyasa
Yayin da mahalarta taron koli na kungiyar G8 suke da bambancin ra'ayoyi kan batun Syria, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a ranar 18 ga wata a nan birnin Beijing cewa, kamata ya yi bangarorin da abin ya shafa su tsaya tsayin daka kan manufar warware batun Syria ta hanyar siyasa da kuma yin kokarin daidaita bambancin ra'ayoyinsu.
Hua Chunying ta kara da cewa, a halin yanzu, an shiga lokaci mai muhimmanci ne wajen warware batun Syria ta hanyar siyasa. Aikin dake gaban kome shi ne sa kaimi da a gudanar da taron Geneve karo na biyu cikin hanzari, da magance daukar matakan da za su tsananta rikicin kasar Syria, da kuma taimakawa wajen warware batun na Syria yadda ya kamata. (Zainab)