in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi kiran da a nuna adalci game da batun amfani da makamai masu guba a rikicin Syria
2013-06-14 20:26:34 cri
Kakakain ma'aikatar harkoin wajen kasar Sin Hua Chunying ta fada a ranar Jumma'a cewa, kasar Sin tana fatan hukumar kasa da kasa ta MDD dake bincike game da Syria, za ta nuna gaskiya da adalci, a binciken da ta ke gudanarwa game da zargin amfani da makamai masu guba a rikicin kasar.

Madan Hua Chuinying ta fada yayin taron mamena labarai a Beijing cewa, matsayin Sin game da batun amfani da makamai masu guba bai canja ba kuma a fili yake cewa,ko ma wane ne ya yi amfani da makamai masu guba,Sin ba za ta yi goyon bayan matakin ba.

Fadar Amurka ta White House ta fada cikin wata sanarwa a ranar Alhamis cewa,hukumar leken asirin Amurka ta gano cewa, gwamnatin Syria ta yi amfani da makamai masu guba, ciki har da sinadarin sarin dan kadan kan 'yan adawa a lokuta da dama a shekarar data gabata.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China