in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fitar da sabon shugaban kungiyar jam'iyyun adawa da gwamnatin kasar Syria
2013-07-07 16:56:52 cri
Yayin zaman ranekun 4 zuwa 6 ga watan nan na Yuli, wanda mambobi 114 daga jam'iyyun adawa da gwamnatin kasar Sham suka yi a birnin Istanbul na Turkiya, an fitar da Ahmad Assi Jarba a matsayin sabon shugaban gungun 'yan adawar kasar.

Ahmad Assi Jarba wanda ya fito daga wata kabila dake jihar Hasaka a gabashin kasar ta Sham, yana da alaka mai karfi da mahukuntan kasar Saudiya. Baya ga shi kansa Jarba, an fitar da mataimakansa uku, da wani babban sakatare a taron na wannan rana.

A gun taron na yini uku, an kada kuri'u kan 'yan takara dake burin jagorantar wannan kungiya, inda daga karshe Jarba ya sami kuri'u 55 a zagaye na biyu, matakinda ya bashi damar samun nasara kan abokin hamayyarsa Mustafa Sabbagh.

Mahalarta taron daga jam'iyyun adawa da gwamnatin kasar ta Sham sama da 10, da sojojin da suka bijirewa gwamnati, sun kuma yi shawarwari kan hanyar daidaita rikicin kasar a siyasance.

Bayan taron, tsohon shugaban kungiyar jam'iyyun adawa na wucin gadi ya bayyana wa 'yan jarida, ciki hadda na kamfanin dillancin labarun kasar Sin Xinhua cewa, kungiyar tasu ba za maida hankali kan batun halartar taron Geneva kan batun kasar ta Sham, wanda kasashen Amurka da Rasha suke kokarin kira ba. (Fatima).

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China