A wannan rana, hargitsin da ya abku a Alexandria ya yi sanadin mutuwar mutane 12, yayin da wasu 5 suka rasa rayuka a cikin hargitsin da aka samu a dab da fadar shugaban kasar da ke birnin Alkahira da filin Tahrir. Sa'an nan kuma mutane 5 sun mutu sakamakon hargitsin da aka samu a tsibirin Sinai, yayin da wani ya mutu cikin hargitsin da ya barke a lardin Suez, wani kuma ya mutu cikin hargitsin da ya abku a lardin Asyut.
A ranar 5 ga wata, ta bakin kakakinsa, Ban Ki-moon, magatakardan MDD. ya ba da wata sanarwa, inda ya yi kira ga rundunar tsaron kasar ta Masar da ta hana barkewar hargitsi, da tabbatar da tsaron lafiyar masu zanga-zanga, ya kuma yi kira ga jama'ar Masar da su yi amfani da hakkokinsu cikin ruwan sanyi.
Sanarwar ta ce, kamata ya yi dukkan jama'ar kasar ta Masar su tsai da kuduri kan makomar kasarsu bisa ka'idar girmama banbance-banbance na ra'ayin siyasa, kana a danka wa shugabannin kasar nauyin shirya wata tattaunawar dimokuradiyya cikin lumana, inda kowa da kowa zai iya halarta.(Tasallah)