in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fadar shugaban Masar ta amince da El-Baradei a matsayin mataimakin shugaban kasar
2013-07-08 09:58:38 cri

Mai baiwa shugaban kasar Masar shawara kan harkokin watsa labarai Ahmed al-Mislimani, ya shaidawa gidan talabijin na kasar a ranar Lahadi da yamma cewa, fadar shugaban kasar ta amince da El-Baradei a matsayin mataimakin shugaban kasa, yayin da shi ke kuma Ziad Bahaa-Eddin, wani kwararre kan harkokin kudi, aka gabatar da sunansa a matsayin firaministan wucin gadi.

Ya ce, an cimma yarjejeniya ce kan wadannan mukamai guda biyu da ake sa ran bayyanawa cikin sa'o'i 24, a kokarin da ake na kafa kyakkyawar gwamnati da ke kunshe da kwararru, ta yadda za ta magance matsalolin da kasar ke fuskanta.

Mislimani ya ce, an fara yunkurin shirin nan na sasantawa tsakanin magoya bayan Mohammed Morsi da 'yan adawa, amma wasu bangarori ba su son ganin wannan mataki ya kai ga gaci.

Ko da ya ke a ranar Asabar da yamma, an yi ta rade-radin cewa, an nada El-Baradei a matsayin firaministan kasar, batun da Mislimani ya karyata. duk da cewa, jam'iyyar Al-Nour mai tsattsauran ra'ayi ta 'yan Salafiya ta ki amincewa da nadin nasa domin ya jagoranci gwamnatin wucin gadin. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China