Majalisun dokokin kasashen Senegal da Cote d'Ivoire sun bayyana babban fatansu na ganin an samu cigaba ta fuskar tsaro bisa ga rikicin arewacin kasar Mali, in ji wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis bayan wata ziyarar aiki a birnin Dakar na Senegal ta shugaban majalisar dokokin kasar Cote d'ivoire, Guillaume Soro.
Bangarorin biyu, a cewar wannan sanarwa, suna ba da kwarin gwiwa ga shugabannin kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ga taimakawa kasar Mali wajen ganin an gudanar da zaben shugaban kasa a cikin watan Yuli yadda ya kamata cikin adalci da zaman lafiya.
Haka kuma bangarorin biyu sun dauki niyyar shirya wani taron karawa juna sani kan shawagin kananan makamai a wannan shiyya tare kuma da ba da goyon baya zauren majalisun biyu da su kafa da tafiyar da harkokin dandalinsu na abokantaka.
Baya ga haka, majalisun biyu sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimta da ta shafi matakai da hanyoyin aiwatarwa da kuma dangantaka tsakanin hukumomin majalisun nasu biyu. (Maman Ada)